Mun zauna da turji munyi masa nasiha – Sheikh Musa

EDITA.
Sheikh Musa Yusuf Assadussunnah ya bayyana cewa ganawar da su ka yi da shugaban ‘yan bindiga Bello Turji da rundunar sa ba ƙaramin abin tsoro ba ne, amma sun yi hakan ne domin ceto al’umma.
Malamin ya ce sun yi wa Turji da yaran sa nasiha, sun faɗa musu gaskiya kan ayyukan da suke yi, tare da tunatar da su muhimmancin jin tsoron Allah. A cewar sa: “Mun yi musu wa’azi, su ma sun faɗi nasu. Idan akwai wanda ke ganin shi ne namiji, to ya je ya faɗa musu gaskiya a gaban su.”
Sheikh Assadus-sunnah ya bayyana cewa ko da yake sun shiga haɗari domin gyara al’umma, wasu mutane da ke zaune a cikin gari ba sa ganin wannan ƙoƙari, sai dai su riƙa sukar su da zagi.
Ya kara da cewa yana da matuƙar wahala a fahimtar waɗan da basu fuskanci irin waɗannan matsaloli ba, amma su ke sukan waɗanda ke ƙoƙarin kawo sauyi.