Security

Gwamnatin tarayya ta kara wa’adin neman aiki a hukumomin tsaro

Hassan Turaki.

Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta bayyana ƙarin wa’adin makonni ɗaya ga waɗanda ke son neman aiki a ɗaya daga cikin manyan hukumomin tsaro na ƙasar. Hukumomin da lamarin ya shafa sun haɗa da Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), Hukumar Tsaro ta Civil Defense (NSCDC), Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS), da Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa (FFS).

A cikin wata sanarwa da Sakataren Kwamitin Hukumomin, Manjo Janar Abdulmalik Jibril (mai ritaya) ya fitar a Abuja, an bayyana cewa an dage rufewar shafin neman aikin da aka tsara a ranar Litinin, 4 ga Agusta, 2025 zuwa Litinin, 11 ga Agusta, 2025. Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin na da nufin bai wa ƙarin masu sha’awar shiga aikin dama su cika takardun neman aikin su yadda ya kamata.

Kwamitin ya jaddada cewa hanyar neman aikin ita ce ta ziyartar shafin su na yanar gizo mai adreshi kamar haka:

https://recruitment.cdcfib.gov.ng,

Kwamitin ya kuma yi gargadin jama’a da su guji zamba ko shiga shafukan bogi. Har ila yau, Manjo Janar Jibril ya nanata cewa dukkan tsarin ɗaukar aikin kyauta ne gaba ɗaya kuma za a gudanar da shi cikin gaskiya da adalci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button