News

Gidan yari me shekaru 100 zai koma gidan tarihi …

Hassan Turaki.

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirin ta na sauya gidan yari na Kurmawa mai tsawon shekaru 100 zuwa gidan tarihin al’adu.

Idan za a iya tunawa cewa gidan yarin Kurmawa, wanda gwamnatin mallakar turawan mulkin mallaka ta gina a shekara ta 1910, yana cikin harabar fadar Sarkin Kano, kuma an tsara shi ne domin rike fursunoni 690. A tsawon shekaru 115 da suka gabata, ya zama daya daga cikin alamomin tarihi da suka shafi zamanin mulkin mallaka da tsarin gyaran hali a jihar Kano.

Jaridar Guarantee ta rawaito cewa Mai ba Gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Alhaji Ibrahim Adam, ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook da aka tabbatar. Ya ce aikin gyara al’adun tarihi na Kano zai hada da kwashe fursunonin da ke gidan yari na Kurmawa zuwa sabon gini da ke Janguza, kusa da barikin sojoji a kan titin Kano–Gwarzo–Dayi.

Ya kara da cewa kididdigar da ake da ita ta nuna cewa sabon gidan yarin da gwamnatin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gina a Janguza, na da damar karbar fursunoni har 3,000.

“Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta kwashe dukkan fursunonin da ke gidan yari na Kurmawa zuwa Janguza, yayin da za a sauya Kurmawa zuwa gidan tarihin da zai rike kayan tarihi da al’adun gargajiya na jihar,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button