News
KOLMANI: Tawagar jihohin Bauchi da Gombe sun ziyarci rijíyoyin man fetur

Abdullahi Idris.
Tawagar jihohin Bauchi da Gombe sun Kai ziyarar ran gadi, wajen da akeyin rijiyar Mai na Kolmani a ranar asabar din
Tawagar karkashin jagoranci, Kwamishinan ma’aikatar Ma’adinai da Albarkatun kasa na jihar Bauchi, Hon Muhammad Mai wada Bello da takwaran sa na jihar Gombe, Hon Sunusi Ahmad pindiga.
Ziyarar dai nada nufin Sanin halin da Ake ciki, biyo bayan korafe-korafe da aka samu daga al’umomin yankin na Ganin yadda Ake fita da kayayyakin da ake aikin.