Politics

Shugaban Karamar Hukuma ya samar da wutar lantarki ga Ofishin Hukumar lafiya Matakin Farko

Naziru Hamisu.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Ɓaɓura Alh. Hamisu muhd garu ya kawo karshen matsalar wutar lantarki a ofishin hukumar lafiya a matakin farko.

Hamisu garu ya ce ya samar da wutar lantarkin ne a wani mataki na inganta tsaro da kuma samun nasarar gudanar da ayyuka cikin sauki.

Ya bukaci Ma’aikatan hukumar lafiyar yanki da su cigaba da Jajircewa wajen gudanar da ayyukan su domin samun nasarar da ake bukata.

Alhaji Hamisu ya bada tabbacin cigaba da bada hadin kai da goyan ga Hukumar lafiya, tare da barin kofar sa a bude domin karbar Shawarwarin da zasu ciyar da yankin gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button