News
Shugaban Karamar Hukumar Babura, Malam Hamisu Muhd Garu ya samar da wutar lantarki ga Ofishin Hukumar lafiya Matakin Farko
Shugaban Ƙaramar Hukumar na Ɓaɓura ya ce ya samar da wutar lantarkin ne a wani mataki na inganta tsaro da kuma samun nasarar gudanar da ayyukan cikin nasara
Ya bukaci Ma’aikatan hukumar lafiyar yanki da su cigaba da Jajircewa wajen gudanar da ayyukan su domin samun nasarar da ake bukata.
Alhaji Hamisu Muhd Garu ya bada tabbacin hadin kai da goyan ga Hukumar lafiyar, tare da barin kofarsa a bude domin karbar Shawarwarin da zasu ciyar da yankin gaba.
Naziru Hamisu Unguwar Shuri