Politics

RANAR DIMOKRADIYYA: Galadiman Bauran dutse ya mika sako ga al’uma …

Hassan Turaki.

Shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Jigawa Dr. Nasir Sabo Idris ya mika sakon sa na ranar dimokraɗiyya ga daukacin al’umar jihar Jigawa.

Dr. Nasir ya cikin sakon sa da ya rubuta ya aike wa manema labarai ya ja hankalin al’uma musamman matasa da su kiyayi amfani da kalamai na cin mutunci da tozarci ga shugabanni domin tsaftace iyayen gidan su.

Galadiman bauran dutse yace dole ne matasa musamman masu kare muradun iyayen gidan su su tabbatar suna bayyana ayyukan cigaba da akayi wa al’uma domin inganta rayuwar su memakon cin mutuncin masu mutunci.

Ya kara da cewa Gwamna malam Umar A. Namadi yana iya bakin kokarin sa ganin ya sabunta jihar Jigawa da ayyukan raya kasa dan haka akwai bukatar a cigaba da taya shi da adduo’in fatan alkhairi kamar yadda aka saba.

A karshe shugaban hukumar tattara kudaden shiga ya yaba wa al’ummar jihar ganin yadda suke bada hadin kai wajen biyan haraji wanda haka ne yasa aka samu gagarumin cigaba a bangaren tattara kudaden shiga, yayi kira ga jama’a da su kara bada hadin kai wajen biyan kudaden haraji kasancewar da hakane za’a tallafa wa gwamnatin jihar wajen cigaba da wanzar da ayyukan da tasa a gaba ba tare da jinkirtawa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button