DST: Galadiman bauran dutse ya sanya farin ciki a zukatan jama’a …

Hassan Turaki.
Al’umma sun kasance cikin farin ciki sakamakon rabon kudade da suka samu daga shugaban Hukumar tattara kudaden shiga na jihar Jigawa Dr Nasir Sabo Idris fca, Galadiman bauran dutse.
Shugaban Hukumar tattara kuÉ—in haraji na jihar Jigawa DR. NASIR SABO IDRIS fca ya tallafa wa al’uma domin shigowa ayi walwala a lokacin bikin sallah babba.
Galadiman bauran dutse Dutse yayi rabon tallafin sallah Ga mutanan dake karamar Hukumar Dutse. Wanda aka Rabawa sun kama Daga kan shugabanin mazabu su Goma shadaya(11) kowanne su ya rabauta da Naira Dubu talatin (30,000), sai kuma mataimakan su Suma sun rabauta da Naira Dubu Ashirin(20,000) ,sai kuma sakatarorin su suma sun dace da Naira Dubu Ashirin (20,000) kowannen su.
Haka kuma Galadiman bauran dutse ya waiwayi Co-ordinators Na Danmodi support for transformation da Naira Dubu Ashirin (20,000) kowannen su, sai kuma state Exco Na Danmodi support for transformation (DST) sun rabauta da Naira Dubu Ashirin (20,000), da kuma Women leaders na mazabu Suma sun rabauta da Naira Dubu Ashirin (20,000) kowanne su. Sai kuma masu bukata ta musamman.
Galadiman bauran dutse ya baiwa yan “social media” masu yi masa hidima Naira dubu goma 10,000 kowannen su,
Dr. Nasir Sabo Idris yayi kira ga al’umma da su kara baiwa malam Umar Namadi hadin kai domin cigaba da wanzar da ayyukan alkhairi tare addu’ar ALLAH ya kara ciyar da jihar Jigawa gaba.
A karshe jama’a da dama sunyi masa addu’ar ganin cigaba a cikin rayuwar sa haka kuma sunyi kira ga mai girma Gwamnan jama’a Mal. Umar A. Namadi da ya kara rike jajirtaccen dan siyasa irin Galadiman bauran dutse.