HAJJ 2025: Maniyyatan Jigawa sun kammala aikin Umrah …

Alh. LUKMAN MALAM. HASSAN
Maniyyatan Jihar Jigawa 930 sun kammala gudanar da aikin Umarah cikin Koshin lafiya a Birnin Makkah.
Darakta Janar na Hukumar jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga jami’in hulda da Jama’a
na Hukumar a Makkah.
Alhaji Ahmed Umar Labbo, yace Maniyyatan sun kammala gudanar da Ibadar Umarah cikin yanayi na farin ciki da annashuwa da kuma koshin lafiya, tare da managartan tsare- tsare na samar da abinci sau uku a rana ga kowane Maniyyaci.
Ya kara da cewa tuni aka samarwa Maniyyatan masaukai kusa da Harami domin samun damar gudanar da ibada, wanda hakan yasa Jigawa ta yi fice a tsakanin takwarorin ta.
Darakta Janar na hukumar ya kuma Jaddada kudurin hukumar na ci gaba da kula Maniyyatan domin samun damar gudanar da aikin Hajji cikin nasara.
Daga nan ya bayyana irin nasarorin da hukumar take samu a tun daga nan gida Najeriya har zuwa kasa Mai Tsaki, a matsayin ni’ima daga Allah Madaukakin Sarki.