HAJJ 2025: Malamai sun yaba ma gwamna …

LUKMAN MALAM HASSAN.
Tawagar kwamatin Malaman addini na Jihar Jigawa ya yabawa Gwamnatin Jiha bisa samar da Kujerun aikin Hajji 37 ga Malamai domin fadakar da maniyyata kan aikace-aikacen aikin Hajji.
Sakataren Kwamatin, Dakta Abdulkadir Saleh Kazaure ya bayyana haka ta cikin shiri Hajji Mabrur a birnin Madinah
Ya ce an samar da Malami a kowace karamar hukuma bisa la’akari da falalar aikin Hajji.
Dakta Abdulkadir Saleh Kazaure ya kara da cewa wannan tsari yasa Jihar Jigawa ta yi fice a tsakanin takwarorinta Wanda a duk Najeriya babu Jihar ta dauki Malamai 37 sai Jigawa, inda tuni tawagar ta jagoranci raka maniyya dukkanin muhimman wuraren ziyara a Madinah.
Sakataren Kwamatin ya kuma jaddada kudurin Malaman na ci gaba da fadakar da maniyyata tare da bukatar addu’o’i na musamman ga Gwamnatin Jiha.
Daga nan ya godewa Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa jajircewa da kuma sadaukarwa domin samun nasarar aikin Hajjin bana.