DAMFARA: An kama masu canjin dalar bogi a birnin kudu …

HASSAN TURAKI.
Rundunar yan sandan jihar Jigawa tayi nasarar cika hanu da wasu mutane wadanda sukayi sansani a jejin birnin kudu suna kiran mutane a waya da yaudarar basu dalolin kudade a matsayin canji cikin farashi me rahusa kamar yadda wasu mutane suka kai rahoto ofishin yan sanda cewa wasu mutane sun yaudare su zuwa cikin jeji da yarjejeniyar basu canjin dala a farashi me sauki na kuɗin Nigeria.
Bayan samun wannan rahoto ne, hukumar yan sanda tare da hadin gwiwa da Yan bulala suka shiga jejin kuma sukayi kwanton bauna suka cafe wasu masu suna Halilu Da’u, da Abubakar Abdullahi da Muazu Aliyu da Mu’azu Garba duka yan kauyen Sindimina dake karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.
Yayin gudanar da bincike an same su da Dalar Amurka ta bogi da ta kai dari daya da sittin da uku na yan dari-dari sababbi.
Tuni dai aka garzaya dasu sashin bincike na babban ofishin yan sanda dake birnin dutse domin gudanar da bincike kuma za’a mika su gaban kuliya da zarar an kammala bincike kamar yadda Kwamishinan yan sandan jihar Jigawa CP. AT Abdullahi ya tabbatar wa manema labarai a yayin ganawar sa dasu a babban ofishin yan sanda dake dutse babban birnin jihar Jigawa.