LAMIDO: Na baiwa yar’adua shawara Inji Sule LAMIDO

Hassan Turaki.
Tsohon Babban Sakatare na jam’iyyar SDP, kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa marigayi Shugaban Ƙasa Umaru Musa Ƴar’Adua ya ƙi bin shawarar da ya ba shi, sannan ya amince da cewa zaɓen 2007 da ya kawo shi mulki cike yake da maguɗi da kura-kurai.
Wannan yazo ne a wani ɓangare na tarihin rayuwarsa da aka wallafa mai suna “Being True to Myself”, wanda aka saki a ranar 13 ga watan Mayu da muke ciki, Lamido ya bada labarin yadda ya shawarci Ƴar’Adua da ya sauya kalmomin da yake shirin amfani da su a gaban taron Majalissar Ƙasa ta Jihohi. Lamido ya bashi shawarar ya cewa: “duba da buƙatar gyaran tsarin zaɓen mu,” maimakon yace: “duba da ɗimbin kura-kurai da aka samu a zaɓen da ya gabata.”
Amma a babi na 11 na littafin da aka sanya wa suna “The Yar’Adua Presidency”, Lamido ya ce Yar’adua ya nace a kan maganar sa kuma ya bayyana cewa zaɓen da ya kawo shi mulki an gudanar da shi cikin “maguɗi mai tarin yawa.”
Lamido ya bayyana cewa wataƙila wannan takarda ita ce ta zama tushen tsamin dangantaka tsakanin Shugaba Obasanjo da Shugaba Yar’Adua.