SIYASA: Wani matashi ya fara tattaki daga Jigawa zuwa Kano …

Hassan Turaki
Tuni dai dan gwagwarmayar siyasa Lawan Habibu ya kama hanyar Kano daga birnin dutse ta jihar Jigawa domin yin tattaki da niyyar karrama Gwamna abba Kabir Yusuf na jihar Kano bisa dalilai guda biyu.
Lawan wanda ya shahara a harkar kirkirar sabon salon siyasa dake tada kura a fagen siyasa ya dauki wannan aiki ne domin gani Gwamna Abba ya jinjina masa dangane da yadda yake karrama dan adam kamar yadda yace.
Haka kuma yace gwamnan na Kano yana da wani hali me kyau da ya cancanci yabo kuma zai bayyana wa jama’a da zarar ya shiga birnin dabo.
Da yake amsa tambayar manema labarai jim kaɗan bayan fitar da daga birnin dutse a kan hanyar sa yace zai jure ruwa da rana da sanyi gami da zafin rana domin cikar burin sa.
Labarin zai cigaba …..