HASSAN TURAKI.
Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin gaggauta yin garambawul ga dabarun tsaron kasa, inda ya bukaci daukar matakin gaggawa don kawo karshen tashe tashen hankula a jihohin Borno, Benue, Plateau da Kwara.
Shugaban wanda ya gana da shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa dake Abuja na tsawon sa’o’i biyu, yace dole ne a daina kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba a jihohin Borno, Benue da Filato.
Shugaba Tinubu yayin da ya sake yin alla-wadai da hare-haren rashin imani da ake kai wa ‘yan Najeriya.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, yace hafsoshin tsaron sun yi wa shugaban kasa bayanin duk hare-haren da aka kai a jihohin, da yawan mace-macen da aka yi, da kuma lalata dukiyoyi.
Ribadu ya lura cewa, shugaba Tinubu ya kuma tabbatar da sa ido sosai tare da bayar da umarni yayin ziyarar aiki da ya kai Paris da Landan.
Ya kuma kara da cewa maharan kan afkawa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ta hanyar dasa abubuwan fashewa da kuma kai hare-hare a yankunan da zuwan jami’an tsaro na ɓata lokaci.
Leave a Reply