HAUWA SANI.
Jami’an ‘yan sandan Legas sun kama wani mutum da ake zargin ya kashe mahaifinsa tare da daddatsa gangar jikin mahaifin nashi…
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani matashi dan shekara 24 mai suna Sowe Temidayo Igbekele da laifin kashe mahaifinsa mai suna Babatunde Sowe Kayode mai shekaru 60 tare da daddatsa gangar jikinsa a gidansu da ke unguwar Oshodi a jihar.
Majiyar ‘yan sandan ta shaida cewa, an kama wanda ake zargin ne a ranar Lahadin da ta gabata, biyo bayan rahoton da wata ‘yar uwarsa mai suna Temidayo Akinola da ke lamba 56 a kan titin Igbehinadun, a Oshodi ta kai sashin Alakara a ofishin ‘yan sanda.
A cewar majiyoyin, lamarin ya faru ne a ranar 17 ga watan Afrilu da misalin karfe 9:00 na safe a cikin gidan. Har yanzu ba a tantance musabbabin wannan mugun aikin ba.
Ya ce tawagar masu binciken kisan gilla sun ziyarci inda lamarin ya faru tare da daukar hoto, yayin da aka kwashe gawar mamacin da aka daddatsa aka ajiye a dakin ajiyar gawa na jama’a don tantance gawarwakin.
Wanda ake zargin wanda ya gudu daga wurin bayan faruwar lamarin, an bi sawun sa tare da kama shi a maboyar sa da ke Oshodi a ranar 20 ga Afrilu.
Leave a Reply