2027: Na tsine wa jam’iyyar APC, zata lalace – El-rufa’i

HAUWA SANI.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna mal. Nasir El-rufa’i yace ya tsine wa jam’iyyar APC ne saboda lalacewa ta yafi amfani ga duk wani dan Nigeria me kishin kasa.

El-rufa’i ya ambata cewa “Ko Ɗa ka haifa, ka yi iya ƙoƙarin ka, kayi Addu’a, amma ya fanɗare, dole ka tsine masa ka barshi da duniya, don haka na tsine wa jam’iyyar APC na barta da Duniya”

ya kara da cewa babu wata gwamnati me hankali da zata fara neman tazarce a kasa da shekara biyu bayan karbar rantsuwar fara aiki, hakan ya nuna rashin tabbas da dimuwar da jam’iyyar ta shiga sakamakon tsinuwar waliyyan siyasa.

Tsohon gwamnan kuma sabon dan jam’iyyar SDP yace babu makawa shirin kawar da tinubu a mulki ya kankama kawai lokaci ake jira tunda ALLAH baya son zalunci.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *