HAFSAT JINGAU.
Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso yayi kira ga Magoya Bayan sa da Suyi watsi da raɗe-raɗin da yace jam’iyyar Apc take yaɗawa kan cewa zai Shiga cikin jam’iyyar.
Kwankwaso yace “Dana koma jam’iyyar Apc gwanda na haƙura da Siyasa baki ɗaya.
Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa yace Rabi’u Musa Kwankwaso yayi watsi da ikirarin da akeyi cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, na shirin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ya ce jam’iyyar NNPP tana baiwa ‘yan Najeriya fahimtar abubuwan da jam’iyyar zata iya bayarwa ta hanyar gudanar da shugabanci mai cike da gaskiya da rikon amana, ya kara da cewa gazawar siyasa ne kawai ke magana kan zabe mai zuwa a tsakiyar wa’adinsu.
Idan dai za’a iya tunawa a kwanakin baya ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, yayi hasashen komawar Kwankwaso jam’iyyar APC, inda ya jaddada cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na shirin yin tuggu.
Ganduje, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar magoya bayan Tinubu, wadan da suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja, ya bayyana cewa jam’iyyar APC na ci gaba da karbar fitattun ‘yan siyasa ciki har da ‘yan majalisar tarayya.
Leave a Reply