HASSAN TURAKI.
Rundinar ‘yan sandan Jahar Jigawa karkashin jagorancin CP AT Abdullahi, psc, tana sanar da ilahirin jama’ar Jahar Jigawa cewa daga gobe Asabar 19 ga watan April har zuwa 11 ga watan May, 2025, za ta gudanar da atisaye na koyar da harbi ga sabbin kuratan ‘yan sanda.
Za’a yi atisayen ne a garin Tsohon Kafi dake karamar hukumar Birnin Kudu.
Don haka sanarwar take shawartar mutane da su kauracewa wajen sannan kuma su kwantar da hankulan su in sun ji karar harbe-harbe na bindiga a kwanakin da aka ambata.
Muna fatan za’a ci gaba da yin addu’oin dorewar zaman lafiya ga Jahar Jigawa da ma kasa baki daya.
Mai Sanarwa:- SP Lawan Shiisu Adam, Jami’in Hulda Da Jama’a Na Rindinar ‘Yan Sandan Jahar Jigawa Da Ke Birnin Dutse.
Leave a Reply