HASSAN TURAKI.
An bukaci al’uma da su bada hadin kai domin karbar riga-kafin cutar shan inna wato polio.
Wannan na zuwa ne a sati daya kafin fara gangamin wayar da kai dangane da cutar matsaloli dama hanyar kauce wa kamuwa da cutar shan inna.
Anyi wannan kira na yayin wata bita da aka gudanar a Tahir guest palace dake birnin dutse, taron da Gidauniyar lafiya ta UNICEF ta dauki nauyi domin wayar da kan masu gabatar da shir-shirye a gidajen Radio dake fadin jahar Jigawa.
Wakilan Gidauniyar ta UNICEF sun tabbatar da fara gangamin riga-kafi ta duniya daga ranar 24 zuwa ranar 30 na wannan wata cikin satin da zamu shiga.
A ƙarshe, Gidauniyar tayi kira ga kafafen sadarwa da su bada hadin kai wajen isar da sakon UNICEF domin tallafa wa juna wajen kawar da cututtuka da suka addabi jama’a musamman cutar polio
Leave a Reply