ASHIRU GAMBO.
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi FCA, ya jagoranci bikin aza harsashin ginin wata babbar cibiyar kula da lafiya da babu irinta a duk faɗin Najeriya. Wannan cibiyar za ta ƙunshi manyan rukunai guda uku, wato:
-Cryo-Oxygen Plant – Wurin sarrafa iskar oxygen ta hanyar cryogenic distillation.
-Cibiyar Kula da Cututtukan Zuciya (Cardiac Centre)
-Cibiyar Gwaje-gwaje ta zamani (Diagnostic Centre)
A ƙoƙarin da Gwamna Namadi ya ke na ciyar da fannin kiwon lafiya gaba a jihar Jigawa. Tun daga lokacin da ya hau mulki, gwamnan ya kaddamar da manyan ayyuka masu muhimmanci a fannoni da, musamman ɓangaren kiwon lafiya.
Kafin wannan aiki na yau da aka ƙaddamar, gwamnati ta inganta ƙanana asibitoci guda 181 ta hanyar samar musu da kayan aiki na zamani, na’urorin hasken rana, ruwa, da gidajen zama ga ungozoma, wanda duk ya lakume kusan naira biliyan 12.
Haka kuma, an ware biliyan 5 don gina sabon matsugunni na dindindin ga makarantar koyon aikin jinya da ungozoma da ke Hadejia, tare da kashe biliyan 1.9 a kan kwalejin koyar da fasahar jinya ta jihar da ke Jahun. Sauran kudaden da aka kashe sun haɗa da naira miliyan 386 don gyara wasu makarantun jinya da ke Birnin Kudu, Ɓabura da tsohuwar makarantar Hadejia, wanda hakan ya bai wa makarantun damar karɓar karin ɗalibai daga hukumar kula da makarantun jinya ta ƙasa da kuma fara karatun aikin ungozoma a Hadejia.
Gwamnatin jihar, a karkashin jagorancin Gwamna Namadi, ta raba gidajen sauro da magungunan zazzaɓi har guda miliyan 3.2 a faɗin jihar. Haka zalika, mutane sama da 143,500 sun amfana da shirin inshorar lafiya na J-Basic Health Care, wanda ya bai wa masu ƙaramin karfi damar samun magani kyauta. An saka naira biliyan 1 cikin wannan shirin, inda kuma gwamnati ke bayar da magani kyauta ga masu fama da cututtuka kamar hawan jini, ciwon suga, cutar hanta da kuma yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar.
Har ila yau, an bayar da kwangilar gina manyan asibitoci na kwanciya a Kafin Hausa da Ringim da ya kai naira biliyan 9. Sannan an bayar da kwangilar ƙarin gine-gine a asibitocin kwararru na Hadejia da Kazaure a kan naira biliyan 1.2, tare da kashe naira biliyan 2 domin kayan aiki. An kuma kammala aikin asibitin ƙashi na Gumel da kudinsa ya kai naira miliyan 380.
Gwamna Namadi ya kammala aikin manyan asibitocin Gwiwa, Garki, Guri, Gantsa da Gwaram, wadanda tuni sun fara aiki. Haka kuma, an kammala zuba kayan aiki a asibitocin Gagarawa da Kirikasamma. An kuma sanya na’urorin hasken rana a asibitocin Gumel, Hadejia, Babura, Kazaure, Kafin Hausa da Dutse. Akwai kuma aikin gina cibiyoyin wankin koda kyauta guda biyar a fadin jihar.
Gwamnan ya ɗauki sabbin ma’aikatan lafiya kusan 3,000 a matakai daban-daban.
A jawabinsa, Gwamna Namadi ya jaddada cewa manufar wannan katafariyar cibiya ita ce samar da ingantacciyar kiwon lafiya ga al’ummar jihar Jigawa da ma Najeriya baki ɗaya. Cibiyar Cryo Oxygen za ta samar da iskar oxygen ga asibitocin jihar da ma sauran wurare har da kamfanonin sarrafa takin zamani. Cibiyar kula da cututtukan zuciya za ta mayar da hankali ne kan gano da magance cututtuka kamar bugun zuciya, hauhawar jini da kuma karayar zuciya. A Cibiyar Gwaje-gwaje ta zamani kuwa, za a yi amfani da na’urori irin su X-ray, CT scan, MRI, ultrasound da kuma gwaje-gwajen jini da fitsari, domin gano cututtuka ciki har da cutar daji da sauran cututtuka masu yaduwa.
Gwamnatin jihar za ta haɗa gwiwa da masu zuba jari don gudanar da wannan cibiya domin bunƙasa kiwon lafiya, habaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Ya kuma bukaci ma’aikatan lafiya da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu bisa gaskiya da rikon amana, domin gwamnati ba za ta lamunci wasa da aiki ba. A ƙarshe, ya gode wa abokan haɗin gwiwa kamar UNICEF, WHO, FCDO, USAID, Bill and Melinda Gates Foundation da sauran kungiyoyi da manyan malamai da sarakunan gargajiya bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban kiwon lafiya a jihar.
-Malam Garba Al-Hadejawy FIMC, FCAI, FCIFC
Special Assistant to the Governor
(New Media)
Leave a Reply