SIYASAR KANO: Fa’izu Alfindiki ya fadi ra’ayin sa …


EDITA.

Kamar yadda ya wallafa a shafin sa na facebook Fa’izu Alfindiki yace ;

In banda son zuciya irin na yan Kwankwasiyya basu ma shigo jam’iyyar APC ba amma har sun fara yunkurin raba Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da Kujerar sa !

Babu wanda duk Najeriya ya kawowa Shugaban Kasa Bola Tinubu kuri’u kamar Dr. Abdullahi Umar Ganduje a zaben shekarar 2023 !

In ma da gaske za’a sauya Kashim Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa a zaben shekarar 2027, wa yafi cancanta tsakanin Ganduje da Kwankwaso?

Bama goyon bayan sauya Kashim Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa a zaben shekarar 2027.

Tun yan Kwankwasiyya basu shigo jam’iyyar APC ba amma sun fara kokarin raba kan yan jam’iyyar APC a matakin Tarayya balle abinda zasuyi na kawo rudani da hargitsi a Jam’iyyar APCin Jihar Kano.

In har yan Kwankwasiyya zasu sake shigowa jam’iyyar APC dole a gindaya musu sharuda masu tsauri ciki har da batun ba za’a basu takarar kujerar Gwamna a zaben shekarar 2027 ba.

Jam’iyyar APC bata bukatar Kwankwaso da yan Kwankwasiyya dan sake lashe zaben Shugaban Kasa a shekarar 2027.
Kazalika jam’iyyar APCin Jihar Kano cikin sauki zata karbe mulkin Jihar Kano daga hannun yan Kwankwasiyya.

Kanawa sun gaji da mulkin Kwankwasiyya da tarihin da suka kafa bai wuce na Rusau da Rushe Masarautu ba. Kanawa na fatan jam’iyyar APCin Jihar Kano ta karbi mulkin Jihar a zaben shekarar 2027 dan sake hade kansu da samar da ayyukan cigaba da bunkasar tattalin arziki.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *