Shekaru 18 kenan da Kisan Shiekh Ja’afar …

Ibrahim A. makama.

A Ranar 13 Ga Watan Afrilu 2007 Wanda Yazo Dai-dai Da Ranar juma’a 26/Rabii’u Awwal/1428 Allah Ya Karbi Rayuwar Shiekh Ja’afar Mahmud sakamakon harin da wadansu ‘yan ta’adda suka kai masa, a dai-dai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma’a na Dorayi.

Ya rasu ya bar mata biyu, da ‘yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 dai-dai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa.

Marigayin yana daya daga cikin manyan malaman addini a bangaren mabiya Sunnah da ke da dimbin magoya baya. Duk da cewa har yanzu jama’a na ci gaba da bayyana mutuwar sa a matsayin wani babban rashi, amma kuma har yanzu babu wani da aka kama da laifin kisan malamin.

Sai dai a wani bidiyo da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fitar a watan Fabrairun 2020 ya yi nuni da cewa su ne suka kashe malamin.

Kararuttukan Sheikh Ja’afar, musamman na Tafsirin Al-Kur’ani, sun yadu a sassan duniya, kuma har yanzu yana samun yabo game da zurfin iliminsa da iya bayani a saukake gami da amfani da kyawawan lafazin da kuma iya mu’amala.

Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya zama babban abin koyi ga dalibai da malamai musamman ganin yadda ba ya shakkar tsage gaskiya cikin hikima. Malam bai bar shugabanni ba, bai bar masu sarautar gargajiya ba, haka kuma bai bar ma’aikatan gwamnati ba, bai bar ‘yan kasuwa ba, kamar yadda bai bar talaka ba.

Malam ya rasu ne a wani lokaci da al’ummar Musulmi take buƙatar malami irin sa. A lokacin da mafi yawan malaman makarantun suka zama makwadaita, shi Malam Ja’afar sai ya zama daban, ya zama wanda ya san kansa kuma ya rike mutuncin kansa.

A lokacin da malaman suka siffantu da karkatar da mabiyan su saboda neman girma da neman abin duniya, Malam Ja’afar ya sami kaifi daya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *