HASSAN TURAKI.
Rundunar Ƴan sanda ta babban birnin tarayya Abuja ta fara bincike kan sace wata mota ƙirar Toyota Hilux mai launin baƙi mallakin Ofishin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro ONSA, Nuhu Ribadu, wadda aka sace yayin da ake cikin sallar Juma’a a Abuja.
Majiyoyi sun bayyana cewa an ajiye motar ne da ƙarfe 1:05 na rana a gaban ginin hukumar kula da yankin Abuja Municipal Area Council AMAC dake Area 10, yayin da Ribadu ya halarci sallah a wani masallaci. Bayan ya dawo daga sallah, jami’in ya tabbatar wa Ribadu cewa motar ta bata bat kuma sace motar akayi.
Ƙwararren masanin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana faruwar lamarin a shafinsa na Twitter, inda ya ce an kai rahoton sace motar ga ofishin ƴan sanda na Garki a kusan ƙarfe 2:00 na rana, wanda hakan ya janyo hanzarin martani daga hukumomin tsaro.
A sakamakon haka, rundunar ƴan sandan Abuja ta ƙaddamar da bincike ta hanyar tsayawa da duba ababen hawa a wurare daban-daban na shiga da fita a birnin.
Leave a Reply