ASHIRU GAMBO.
Rundunar ƴansandan jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekara 50, bisa zargin yi wa ƴarsa ciki a ƙauyen Kurmi Ado da ke ƙaramar hukumar Ganjuwa a jihar.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Ahmed Wakil ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce rundunar na shirin gurfanar da shi a gaban kotu.
Rundunar ƴan sanda tace tana zargin mutumin mai shekara 50 da cewa ya riƙa yi wa ƴar tasa mai shekara 17 fyaɗe, lamarin da ya sa har ta kai ga ɗaukar ciki.
SP Wakil ya ce bayan samun rahoton zargin ne rundunar a fara gudanar da bincike tare da kama mutumin.
Kakakin ƴan sandan yace a lokacin da ake yiwa magidancin tambayoyi ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi, inda kuma binciken likitoci ya tabbatar da cewa ya jima yana lalata da yarinyar, inda yake haka take ɗauke a cikin wata uku.
SP Wakil ya ƙara da cewa a lokacin da ƴan sanda ke yi wa yarinyar tambayoyi ta tabbatar da tuhumar mahaifin nata, tana mai cewa lamarin ya faru ne a lokacin da mahaifiyar ta tayi bulaguro zuwa wajen dangin ta.
A lokacin da mahaifiyar ta dawo ne ta fahimci ƴar tata na da ciki, inda bayan ta tuhumeta tace mahaifn ta ne yayi mata, kamar yadda ƴan sandan suka bayyana.
Leave a Reply