OBI: Talauci yayi wa yan nijeriya katutu …

HASSAN TURAKI.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce talauci a Najeriya ya tsananta matuƙa har ta kai mutanen da suka saba bada abinci a baya yanzu suna neman taimako daga wajensa.

Obi, ya bayyana hakan ne a lokacin taron kwamitin zartarwa na ƙasa na jam’iyyar LP da aka gudanar a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja a ranar Laraba.

Obi yace “Najeriya na rushewa. Lamarin tattalin arziƙi na ƙara taɓarɓarewa, mutane na ƙara shiga cikin talauci kullum”.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *