ASHIRU GAMBO.
Gwamnatin jihar Bauchi karkashin gwamnan jihar Sanata Bala Muhammad tayi umarnin mallaka wa almajiran marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen tanshi filin idi na Games Village dake cikin garin bauchi.
An dade ana taƙaddama tsakanin marigayi Mal. Idris dutsen tanshi da gwamnatin jihar akan wannan fili wanda kusan shine Ummul aba’isun takun saka da ya sarqe tsakanin marigayin da gwamna Bala.
Mutane da dama sunyi mamakin yadda gwamnan ya mallaka wa kwamitin masallacin Idris Abdul’aziz wannan fili cikin alhini yayin gabatar da jawabin ta’aziyya a gidan malamin.
Leave a Reply