Abunda AIG yayi cin fuska ne ga masarautun arewa …

BY EDITOR.

“Gayyatar Da Rundunar ‘Yan Sanda Suka Yi Wa Sarki Sanusi II Cin Fuska Ne Ga Masarautun Arewa” Barista Nuhu Dantani

Ni a fahimta ta, Wannan cìn mutunci ne ga ilahirin mutanen Arewa ba kawai Kano ba. Hatta sarautar gargajiya na ilahirin Arewa.

Duk da ‘ýan sanda suna da damar gayyatan kowaye a Nijeriya idan dai har ana tuhumar shi da wani laifi amma ya kamata a yi abu cikin adalci da kuma mutunci kamar yadda yazo a doka.

Wasu za su yi murna, amma wannan abunda IGP ya keyi cin mutunci ne ga Sarautar Gargajiya dama arewacin najeriya.

Don haka ina mai rokon shugaban ‘yan sanda na kasa da ya sake yin duba da wannan wasikar gayyatar, ya kuma samo wata hanya ta magance wannan matsala a hukumance a tsarin doka.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *