POLICE: An sauya wa AIG Gumel ofishi dangane da batun ribas

HASSAN TURAKI.

An sauya wa AIG Usaini Gumel wurin aiki bayan daya bayyana ra’ayin sa dangane da sanya dokar ta baci a jahar Ribas da gwamnatin tarayya tayi.

Babban Sufeton ‘yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun, ya mayar da Usaini Gumel Mataimakin sa dake kula da Yankin Zone 7 Abuja zuwa Sashen Hulɗa da Jama’a, Bincike da Tsare-tsare, bisa zargin cewa ya bayyana ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers da kuma dakatar da Gwamna Sim Fubara a matsayin abin da ya saɓawa kundin tsarin mulkin nijeriya.

An rawaito cewa Gumel ya faɗi ra’ayin sa ne kan dokar ta-ɓaci a cikin ofishin sa yayin wata tattaunawa da wasu daga cikin abokan aikin sa, amma ɗaya daga cikin su ya tona masa asiri ya kai rahoto ga babban Sufeto Janar na yan sandan nijeriya.

An dai tabbatar da dauke Gumel daga Zone 7, wacce ke kula da Babban Birnin Tarayya da Jihar Neja, ke da matakin aiki mai muhimmanci da kuma ɗaukaka, ana kallon Sashen Hulɗa da Jama’a, Bincike da Tsare-tsare a matsayin wuri na ladabtarwa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *