KANO: Gwamnati ta ayyana ranar komawa makarantu

Ashiru Gambo.

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Lahadi, 6 ga Afrilu, 2025, a matsayin ranar komawar ɗalibai makarantu domin fara zangon karatu na uku na shekarar 2024/2025, sanarwar da ta ce ta shafi dukkanin makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, an bukaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci, sanarwar ta kuma yi gargaɗin cewa duk ɗaliban da suka gaza komawa makarantun a ranar da aka ƙayyade za su fuskanci hukunci.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *