Hawan Sallah: Ƴansanda sun sake gayyatar Hadimin Sarki Sanusi

Ibrahim A makama.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin amsa tambayoyi kan zargin saɓa wa umarnin da ƴan sandan suka bayar na haramta Hawan Sallah a Kano.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce rundunar ta jaddada matsayinta na haramta Hawan Salla a faɗin jihar, kuma duk wanda aka samu da laifin saɓa umarnin zai ɗanɗana kuɗar sa.

Kwanaki kafin ranar Sallah ne dai rundunar ƴan sandan jihar ta fitar da sanarwar haramta Hawan Sallah a Kano bayan da ta ce ta samu bayanan sirri na wasu ɓata-gari da ke da aniyar haifar da tashin hankali a lokacin hawan.

Haka kuma sanarwar ta ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya kafa wani kwamitin ƴan sanda mai mambobi takwas domin gudanar da bincike kan tashin hankalin da aka samu a ranar Sallah lokacin da tawagar Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi ke komawa gida bayan jagorantar Sallar Idi.

A lokacin da aka samu hatsaniyar dai an kashe wani jami’in sintiri tare da raunata wani da ke aikin bayar da tsaro ga tawagar sarkin na 16.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *