Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi ya rasu.

Ibrahim A makama.

Wata sanarwa da ta fito daga guda daga cikin iyalansa ta bayyana tabbatar da rasuwar tashi inda ta ce nan gaba za a bayyana lokacin da za a yi masa jana’iza.

Alhaji Abbas Sunusi kawu ne ga Sarkin Kano Muhamamd Sunusi II, kuma mahaifi ga shugaban jamiyyar APC na Kano Alhaji Abdullahi Abbas.

Marigayin shi ne Wamban Kano babban dan majalisar Sarki kafin daga likkafar sarautarsa zuwa Galadiman Kano.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *