KISAN EDO: Ku hukunta su kuma ku biya diyya Inji Abba …

Ibrahim A makama

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kawo ziyarar jaje ga gwamnati Kano da iyalan mafarauta 16 da ɓatagari su ka kone su har lahira a garin Uromi na jihar.

Da ya ke jawabi a gidan gwamnati, Okpebholo ya nuna kaɗuwa bisa lamarin, inda ya tabbatar da cewa 14 eaga waɗanda su ka aikata kisan sun shiga hannu kuma za a tabbatar an yi wa iyalan wadanda aka kashe adalci.

Shi ma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga gwamnan ne Edo da ya tabbatar da an hukunta waɗanda ake zargi.

Gwamna Yusuf ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta baiyana fuskoki da sunayen mutane da aka kama kan kisan gillar, inda ya bukaci gwamnan Edo din da ya tabbatar an biya diyya ga iyalan mamatan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *