HAUWA SANI.
Gwmananjihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da Kwamandan Rundunar Samar da Tsaro a jihar Friday Ibadin, biyo bayan kisan da aka yi wa mafarauta 16 ƴan asalin yankin arewacin kasar nan ranar alhamis da ta gabata.
Sanarwar gwamnatin jihar ta ce an ɗauki matakin ne la’akari da bayanan da ke ƙunshe a rahoton binciken farko da aka gudanar dangane da wannan lamari, wanda ya yi matuƙar girgiza jama’a daga sassan kasar.
Leave a Reply