HASSAN TURAKI.
Me temaka wa gwamna akan harkokin wasanni Hon. Ibrahim Auwal Dutse ya mika sakon sa na Barka da sallah ga mai girma gwamna Mal. Umar A. Namadi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ya raba wa manema labarai a birnin dutse, Auwal yace dole ya gaida sarakunan jihar Jigawa kasancewar su iyayen kasa.
Ya kara da mika sakon gaisuwa ga yan majalissar jihar Jigawa da shugabannin kananan hukumomi da kansilolin su.
Yana me cewa ” Muna godiya ga daukacin al’umar mu duba da adduo’in fatan alkhairi da suke yiwa wannan gwamnati” yana me cewa wannan gwamnati tazo da alkhairai da yawa kuma da sannu kowa zai amfana kamar yadda ake cigaba da samar da ayyukan more rayuwa a ko ina a fadin wannan jiha.
Hon. Ibrahim Auwal ya karkare da addu’ar fatan alkhairi ga jihar Jigawa da kasa baki daya gami da jan kunnen matasa da a zauna lafiya kasancewar zaman lafiya shine ginshikin cigaban kowacce al’uma.
Leave a Reply