HASSAN TURAKI.
yayin gudanar da rabon kayan sallah ga Hakimai na gundumomin
- Jahun digatai 17
- Aujara digatai 28
- Gunka digatai 12
- Kadawawa digatai 13.
Tare da limamai na masallatan juma’a 79 shugaban Karamar Hukumar Jahun Hon Jamilu Muhammad Danmalam ya bayyana rashin Jin dadinsa bisa yanda ake mantawa da iyayen kasa Malaman Addini a irin wannan lokacin Daya kamata a taimakesu.
Yace Yana Daya daga cikin kudurorin sa na shigo da kowanne bangaren Al’umma cikin tsarin shugabancinsa Dan kowa ya anfana
Yace cikin wannan wata na Ramadan ya tallafawa rukunan mutane daban daban
Da suka hadar da
- Masu bukata ta musamman
- Marayu
- Masu karsmin karfi
- Shugabannin jam’iyyar APC
- Ma’aikatan gwamnati
- Mata da Maza.
Da sauran Al’umma kuk ba Dan komaiba sai Dan gudanar da gwamnati da jama’a.
Hon. Danmalam yakama a ake Saka walwala da farin cikin a cikin Al’umma, yayin da kowanne hakimi yasami dinkin sallah na shadda Mai dauke da shakwara, da jamfa, da wando, hade da kudin Abincin sallah.
A nasa jawabin daya daga cikin limamai a karamar Hukumar Jahun mL Yahuza gabari yace a tarihin shugabannin da akayi a karamar Hukumar Jahun ba’a taba samun shugaban Daya kula da limamai da shugabannin Al’umma kamar Hon Jamilu Muhammad Danmalam ba yakuma godemasa isa irin kokarin dayayi, inda ya yimasa Addu’ar samun nasara a lokacin mulkinsa.
Signed:
Ismael Salisu Bature Jahun
Special Assistant on publicity to the
Executive Chairman, Jahun local Government Council.
27-03-2025.
Leave a Reply