‎BINCIKE: Masu sayar da kaji Sunce babu ciniki …

Ibrahim A. makama.

A cewar masu kiwon kaji, a baya irin wannan lokaci na Sallah na kasancewa lokacin da ake samun gagarumin ciniki. Sai dai a bana, suna fuskantar kalubale da suka hada da tsadar abincin su, matsanancin zafi da ke kashe kajin, da kuma karancin masu saye.

‎Duk da haka, masu kiwon kajin  na fatan cewa yayin da Sallah ke kara matsowa, ciniki zai habaka. Isuhu Wada, wani mai kiwon kaji, ya yi kira ga jama’a da su tallafa musu ta hanyar siyan kajin gida, domin ci gaba da raya al’adun Sallah da bunkasa kasuwancin su.‎

Mallam Shuaibu Ismail, wani gogaggen mai sayar da kaji, ya bayyana cewa: “A shekarun baya, zuwa wannan lokaci, mun riga mun sayar da mafi yawan kayayyakinmu.

Amma bana, saye ya ragu sosai, kuma muna cikin damuwa.”Yayin da bukukuwan Sallah ke karatowa, masu kiwon kaji a jihar Kano da kewaye sun koka kan raguwar ciniki, lamarin da ke barazana ga kasuwancinsu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *