Ibrahim A makama.
Mai Martaba Sarki Na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar da hakan Yana Mai bayyana cewa yin hakan ya biyo bayan wasu dalilai.
Yace bayan samun shawarwari da kiraye kiraye daga shugabanni da iyaye da Malamai da Kuma tattaunawa da yan Majalisar Sarki ya zama wajibi a dakatar da hawan Sallah Karama na wannan shekara.
Sarkin yace Hawan Sallah ba abune na ko a mutu ko ayi rai ba, Wanda idan yin hakan zai kawo tashin hankali ko hargitsi da kawo rashin zaman lafiya to ya zama wajibi a hakura dayin hawan.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace ya dauki alkawarin kiyaye Imani da mutunci da dukiya da zaman lafiyar al’uma Wanda hakan ce tasa yaga dacewar daukar wannan mataki domin kaucewa dukkan wani abu daka iya kawo tashin hankali ko rashin samun zaman lafiya a tsakanin al’uma.
A don haka ne Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’uma da sauran masoya suyi hakuri da wannan hukunci da aka zartar domin samun dorewar zaman lafiya a jihar Kano da Kuma kasa baki daya.
Sarkin na 15 yayi amfani da wannan dama wajen kira ga al’uma da suyi amfani da lokutan bukukuwan Sallah wajan ziyartar juna domin sada zumunci, inda ya taya al’umar musulmi murna da farin cikin gudanar da azumin watan Ramadan Yana Mai addu’ar samun dacewar Ubangiji daga cikin bayin sa wadan da Allah yake gafartawa dayin rahama tareda karbar ibadar da aka gudanar.
Leave a Reply