Politics

KANO: Kwamishina ya ajiye aikin sa …

Ibrahim A. makama

Manjo Janaral Muhammad Inuwa Idiris mai ritaya, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kano ya ajiye aikin sa.

Kwamishinan dai bai bayyana dalilan sa na sauka daga mukamin ba a takardar ajiye aikin da ya miƙawa gwamnan.

Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ce gwamna Yusuf ya kaɗu da ajiye aikin da kwamishinan ya yi tare da gode masa kan gudunmawar da ya bayar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button