KANO: Bikin murnar cika shekaru 10 da fara aikin lafiya

Ibrahim A makama

Kungiyar ma’aikatan lafiya matakin farko wadanda tsohon Gwamnan kano Injiniya Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya dauka aiki a shekarar 2015 kimanin mutane 1,107 sun gudanar da taron Addu’oi da Saukar Karatun Alqur’ani mai Girma ga jihar kano da kuma wadanda suka rasu daga Cikin su.

A wani bangare na bikin cikar kungiyar shekaru 10, ta bayar da tallafin kudi 20,000 ga iyalan wasu daga Cikin mambobin su, da suka rasu kafin wannan lokaci kimanin mutane 21.

An gudanar da taron ne a Babban dakin taro na Shalkwatar kungiyar kwadago dake Unguwa Uku a nan kano Karkashin jagorancin shugaban Kungiyar Mukhtar Usaini Bunkure.

Shugaban ya yabawa Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf bisa yanda yake kula da ma’aikatan gwamnatin jihar wajen fitar musu da hakkokin su musamman ta
yanda ya biya ‘yan fansho hakkokin su tare da karin kudi na mafi karancin Albashi ga ma’aikatan gwamnatin jihar.

Inda ya Mukhtar din ya bayyana rashin Jin dadin sa dangane da rashin samun Albashin su na tsawon watanni 8, wasu kuma wata 6, yayin da wasu kuma suke bin Albashin wata 4 daga Cikin ma’aikatan lafiya matakin farko wadanda tsohon Gwamnan kano Rabiu Musa Kwankwaso ya dauka aiki a shekarar 2015.

Wakilin mu ya ruwaito cewar, Mataimakiyar shugaban Kungiyar Hajiya Hauwa Rabo Ibrahim tace, taron wani mataki ne na karfafa zumunci a tsakanin su.

Daga nan tayi kira ga mai girma Zababben Gwamnan kano Injiniya ABBA KABIR YUSUF da ya taimaka ya duba halin da suke ciki na matsin rayuwa akan rashin samun Albashin su na tsawon watanni.

Tana mai cewar, kowa yasan yanda Mata suke da rauni, wasu kuma an bar musu yara marayu, yayin da wasun su kuma suke daukar Dawainiyar gida tare da taimakon iyayen su.

A don haka ta jaddada rokon ta a madadin ‘yan Kungiyar ma’aikatan lafiya matakin farko na jihar kano wadanda tsohon Gwamnan kano Injiniya Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya dauka aiki shekarar 2015, akan ya dubesu ya kawo musu dauki a biya su hakkin su na tsawon watanni 8, wanda har yanzu basu San a ina gizo yake yin sakar ba.

Iyalan Wadanda suka rasu daga Cikin su, sun amfana da tallafin kudin kuma sun bayyana Godiya da kudin da suka samu daga kungiyar ma’aikatan lafiya matakin farko a shekarar 2015.

A karshe sunyi Addu’a ga wadanda suka rigamu Gidan Gaskiya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *