IBRAHIM A. MAKAMA.
Babban mai horar da tawagar Najeriya yan kasa da shekaru 20 Aliyu Zubairu, ya gayyaci dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Barau FC, Ibrahim Yunusa Sulaiman zuwa sansanin daukar horon kungiyar, a shirye shiryen da tawagar ta ke na wakiltar Najeriya a gasar cin kofin Nahiyar Africa yan kasa da shekara 20 da za’a gudanar a kasar Ivory Coast.
Babban mai horarwa tare da tawagar tasa sun kasance a jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya, domin cigaba da gudanar da shirye shiryen tunkarar gasar wacce zata gudana tsakanin 26 ga wata mai kamawa zuwa 18 ga watan Mayu shekarar 2025.
Muna amfani da wannan dama domin taya dan wasa Ibrahim Yunusa Sulaiman murnar samun wannan gayyata, duba da kokarin da yake yi a wannan kaka.
Leave a Reply