HASSAN TURAKI.
A watan Nuwamba na shekara ta 2022, tsohon shugaban karamar hukumar Hadejia, Bala Umar, ya sayi motar ƙirar pickup don jigilar gawarwaki zuwa wuraren binne su, da nufin sauƙaƙe harkar sufuri.
Tsohon shugaban karamar hukumar ya tattara manyan mutane masu daraja waɗanda suka halarci bikin ƙaddamar da aikin motar gawarwaki, inda masu sarauta suka girmama taron, ciki har da Babban Limamin Masallacin Hadejia.
Abin takaici, an yi zargin cewa an canza aikin wannan motar ƙirar pickup zuwa motar kasuwanci kawai don samun kuɗin shiga, yayin da muke da hanyoyi da yawa na samun kuɗin shiga a yankinmu.
Na kira wannan lambar (09036954329) da aka nuna a gefen motar don in nemesu. Abin takaici, direban ya ce an karbe ta kuma an mai da ita ta kasuwanci kawai don samun kuɗi, ba don hidimar ɗan adam ba.
shugaban karamar hukumar Hadejia, Honourable Yaro Abba Ari, mutum ne mai hankali, mai tausayi wanda na san shi tun ina makarantar sakandare.
Duk da haka, waɗanda ke bayan gwamnatin sa ba sa ba shi shawara mai kyau don haɓaka yankin karamar hukumar kamar yadda magabata suka yi.
Hadejia karamar hukuma ce mai faɗi, mai yawan wuraren da za’a iya samun kuɗin shiga akai-akai. To, ME YASA KUKA SOKE KUMA KUKA CANZA AIKIN MOTAR GAWA DAGA AIKIN TA NA YAU DA KULLUM ZUWA NA KASUWANCI KAWAI ?
Idan batun da aka yi na zargin a sama gaskiya ne, wallahi za ku ƙare wa’adin ku ba tare da gudanar da ayyukan ci gaba ba waɗan da zasu amfanar da al’ummar dake ƙarƙashin ikon ku.
Yaro Abba, dole ne ku farka don gyara salon shugabancin ku domin mutane su yaba ayyukan ku.
waɗanda suke da shekaru a cikin majalisar ku, akwai mutane masu hankali da yawa waɗan da zasu iya baku shawara kuma su gabatar da ra’ayoyin ku don ganin an sami nasara.
Daga; Alhaji Musa Muhammad Hadejia.
Leave a Reply