HAUWA SANI.
Tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa idan manyan ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso da Nasir El-Rufai suka haɗa ƙarfi da tunani, hakan na iya haifar da babbar barazana ga jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.
Shekarau ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya ce irin haɗin gwiwar da ake gani tsakanin manyan shugabannin siyasa na iya canza taswirar siyasar Najeriya idan aka yi amfani da ita da hikima da tsari.
A cewarsa, kodayake APC na da wasu ƙarfafun ginshiƙai, haɗin kan waɗannan manyan ‘yan siyasa na iya janyo hankalin jama’a tare da samar da sabuwar hanyar ceto Najeriya daga halin da ake ciki.
Shekarau ya kuma ja hankalin jam’iyyun siyasa da su dage wajen ƙarfafa tsarin cikin gida da haɗin kai, domin samun nasara a babban zaɓen 2027.
A ƙarshe, ya jaddada cewa siyasa na da sauyin yanayi, kuma idan waɗannan manyan jiga-jigan suka zo da tsari da manufa, tabbas za su iya kayar da APC daga mulki.
Leave a Reply