BAUCHI: Gwamnatin jihar Bauchi ta soke hawan sallah …

HASSAN TURAKI.

Gwamnatin Jihar Bauchi ta sanar da soke Hawan Sallah na wannan shekara a Masarautar Bauchi da kewaye.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban mashawarcin gwamnan jihar Bauchi a bangaren yada labarai da Sadarwa Kwamared Mukhtar Gidado.

Gwamnatin Jihar Bauchi tayi bayanin cewa daukar wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kwamitin kula da hawan masarautar Bauchi ya dauka ne na soke hawan ba tare da saka gwamnati a ciki ba, la’akari da tasirin hawan wajen nuna kyawawan al’adun Bauchi da ke jawo hankalin baki zuwa jihar.

Gwamnatin ta kuma bada haƙuri ga jama’a sakamakon halin da zasu samu kansu ciki dalilin daukar wannan mataki.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *