HASSAN TURAKI.
Masarautar Rano ta jaddada kudirin ta na ci gaba da tallafawa ci gaban babban asibitin kwanciya na Rano ta fuskar warware dukkan abubuwan da Kan iya kawo nakasu ga harkokin gudanuwar ci gaban asibitin.
Mai Martaba Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isa Umaru ne ya furta hakan cikin Wani bayani da ya gabatar lokacin da yake amsar bakuncin kungiyar abokai Kan ci gaban babban asibitin kwanciya na Rano karkashin jagorancin shugaban kungiyar Alhaji Nadabo Usman Bunkure yau a fadar sa.
Maimartaba sarki ya kara da cewa yana sane tun tsawon wasu lokuta irin matsalolin da asibitin ke ciki Wanda Kuma ake bukatar wannan kwamati daya sanya ido da nufin ganin an warware irin wadannan matsaloli tare da samun kyakkyawar dorewar kulawar ma’aikata ga marasa lafiya a asibitin musamman ga wadanda akan kawo su cikin dare dan samun kulawar likitoci.
A cewar Mai Martaba Sarkin na Rano wasu lokuta a baya cikin dare an Sha kaiwa marassa lafiya asibitin amma a rasa Wani jami’in lafiyar da zai saurari wannan maras lafiya.
Ya Kuma fadi cewar masarautar na shirye tare da barin kofa bude dan sauraron korafe-korafen jama’a dan warware su.
Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar abokai Kan ci gaban babban asibitin kwanciya na Rano Alhaji Nadabo Usman Bunkure, yace sun ziyarci fadar Sarkin ne da nufin gabatar da kungiyar da nuna goyon baya da Kuma gabatar da ayyukan kungiyar ga Mai Martaba Sarkin na Rano dan neman sanya musu albarka.
Kungiyar ta Kuma godewa Sarkin Rano Muhammad Isa bisa yadda yake tafikar da jagorancin masarautar bisa adalci da kyautatawa al’umma.
A Wani labarin makamancin wannan, Sarkin ya karbi kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa da sauran kungiyoyin wasannin motsa jiki ta Rano karkashin shugabancin Malam Basiru Sani.
Inda suka yiwa Sarkin bayani Kan irin tasirin da kungiyoyin wasannin kenda shi dan bada wakilci na gari ga masarautar kazalika kungiyar ta karrama Sarkin na Rano da takardar shidar girmamawa bisa irin gudunmawar da masarautar ke bawa fannin wasannin motsa jiki.
Da yake jawabi Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isa Umaru ya bukaci kungiyar wasannin data maida hankali wajen wayar da Kan matasa Kan su guji shiga harkokin shaye shaye da aikin dabanci da makaman tansu.
Yace a Mai makon hakan matasa ya kamata su dage wajen samun sana’ar dogaro da Kai.
Sauran kungiyoyin da suka ziyarci Sarkin sun hada kungiyar ‘yan masu hayar babura da mata ‘yan Hisbah da ‘yan siyasa.
Sahannu
Nasiru Habu Faragai,
Sakataren Yada Labaran Masarautar Rano.
Leave a Reply