HASSAN TURAKI.
Dokar ta-ɓaci a Najeriya ba haya ba ce gado ce ta iyaye da kakanni, inda wasu ke ganin an fara amfani da ita ne tun farkon siyasar Najeriya a shekarar 1962 lokacin da aka yi zargin an sami manyan kura-kurai a kidayar jama’a ta farko da aka fara yi a ƙasar har ta kai ga aukuwar shahararren rikicin nan na kungiyar Action Group (AG) wacce tayi tasiri a yammacin Najeriya.
Tarihi ya nuna cewa ranar 1 ga watan Oktoba, firaminista Sir Abubakar Tafawaɓalewa yayi wa al’umar ƙasar bayani yadda ya shaida musu cewa gwamnatinsa tana sane da mugun nufi da wasu ‘yan siyasa masu aniyar kifar da halattacciyar gwamnatin dimokuradiyya da karfin tsiya, har ma tuni suka fara samun horon soji a ƙasashen waje, don haka ya ƙaƙaba dokar ta ɓaci.
Haka kuma ranar 26 ga Oktoba, an tsawaita wannan doka zuwa ga hana tarurrukan jama’a da jerin gwano a daukacin yammacin Najeriya. inda a ranar 2 ga watan Nuwamba ne aka zaƙulo wadan da ake tuhuma 1962, irinsu Cif Awolowo da wasu mutane 26 da suka hada da Anthony Enahoro, Sam Ikoku, Ayo Adebanjo, Lateef Jakande, Alfred Rewane, J.S. Tarka, Josiah Olawoyin, Dr. Oladipo Maja, Bisi Onabanjo, James Aluko, da dai sauransu, abinda a ƙarshe ya kai ga tilasta wa gwamnatin tarayya kafa gwamnatin hadin gwiwa.
Tunda ga lokacin ba a sake jin duriyar dokar ta ɓaci ba sai a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo wanda ya aiyana dokar a ranar 18 ga watan Mayun shekarar 2004 akan gwamnatin jahar Filato da majalisar dokokinta wadda rikicin addini da kabilanci a jahar yayi kamari. Kuma gwamnan jihar Dariye ya kasa kataɓus, Shugaban ya kafa hujja da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin kasa na shekarar 1999 wanda ya sahale masa iya daukan irin wannan mataki.
shugaban ya zargi gwamnan Joshua Dariye da gazawa wajen ganin an kawo karshen rikicin da ya barke tsakanin al’umar Musulmi da Kirista na Jihar Filato wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka sama da 2,000 tun daga watan Satumban 2001.
Sai Shugaba Goodluck Jonathan wanda ya ayyana dokar ta-baci a wasu kananan hukumomi a jihohin Borno da Filato a shekarar 2011 kafin daga baya ya faɗaɗa dokar zuwa jihohin Borno, Adamawa da Yobe sakamakon abinda ya kira ta’azzarar rikice-rikicen ta’addancin Boko Haram a yankin.
Kwatsam ranar 18 ga watan Maris din 2025 ne aka kuma! Inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu yayi amfani da wannan dama da kundin tsarin mulkin kasa ya ba shi a wannan sashe na 305 ya buga gudumar wannan doka a kan jahar Rivers wanda rikicin siyasar ta ya ki ci ya ki cinyewa kusan shekaru biyu da kammala zabubbuka.
Shugaban ya dakatar da gwamna, da majalisar dokokin da ke gaba sa juna wadanda suka hana jahar katabus, har ya buga misali da yadda aka rushe majalisar jahar sukutum kuma aka kasa sake ginawa, ga kuma yadda gwamnati da ma wasu mutane masu zaman kansu suka yi iya kokarin ganin an shawo kan rikicin, amma abin ya gagara.
Sai dai a hanu guda kuma ana ganin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana amfani da karfin mulki ne wajen kwace jihar ribas a hannun babbar jam’iyyar adawa ta PDP kamar yadda wasu ke ganin cewa ya kamata shugaban tun farko ya magance matsalar ta hanya dakatar da hadimin sa Nyeson wike daga sanya baki cikin abubuwan da suka shafi gwamnatin jihar kasancewar lokacin mulkin sa ya wuce, amma yana amfani da shugaban kasa wajen ballo rikici daban-daban a jihar wanda a cikin satin nan wasu fusatattun matasa suka yi zanga-zanga me zafi har takai sun kone gidan sa kurmus a jihar.
Leave a Reply