NLC: Tinubu ka saba layi inji Kungiyar kwadago …

HASSAN TURAKI.

Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC sun yi Allah wadai da abin da suka bayyana a matsayin saba doka da shugaba Tinubu ya yi, wajen kafa dokar ta-baci da dakatar da gwamnan jihar rivers Siminilayi Fubara, da mataimakiyar sa, da yan majalisar dokokin jihar ta Rivers.

GuaranteeNews ta jiyo Kungiyoyin sun ce matakin ya saba wa tanadin sashe na biyu, da sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima, kuma ya zama cin zarafi ga ikon zartarwa.

Cikin wata sanarwa da kungiyoyin suka fitar ranar Larabar nan, sun bukaci shugaban kasar ya gaggauta janye sanarwar da ya bayar, da ka iya dora kasar a kan tubalin sabawa doka a nan gaba, ko su dauki matakin da ya dace.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *