PETER OBI: Tinubu ya cika wa yan Nigeria alkawari …

HASSAN TURAKI.

Tinubu ya cika alkawuran da ya dauka; ya mayar da dala zuwa N1,500, man fetur zuwa N1,000, buhun shinkafa zuwa N100,000 – Peter Obi

Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour a 2023, ya caccaki gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan tabarbarewar tattalin arziki, inda ya dora laifin faduwar Naira, tsadar kayan abinci, da tsadar man fetur akan shugaban.

Yayin ganawarsa da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, Mista Obi ya yi wa gwamnatin Mista Tinubu ba’a, inda ya bayyana cewa ta yi muni fiye da yadda ta hadu da su.

“Tinubu yayi alkawarin cigaba daga inda Buhari ya tsaya. Idan ka duba Buhari ya bar dala a kan kusan N400, yau kusan Naira 1,500. Shinkafa ta kai kusan N40,000, yanzu ta haura N100,000. Man fetur ya kai kusan N300, yanzu ya haura N1,000. Komai ya ninka kuma ya ninka sau uku. Don haka, ya yi daidai kamar yadda ya yi alkawari,” in ji Mista Obi.

Da yake kwatanta tattalin arzikin Najeriya da na Indonesiya, Mista Obi ya ce, “A Indonesia, an rantsar da shugaban kasa kusan lokaci daya da wani a Najeriya. Shekaru 10 bayan haka, Indonesiya ta mayar da GDPn su daga dala biliyan 800 zuwa dala tiriliyan 1.3, kuma yawan kuɗin da kowane mutum yake samu daga dala 3,000 zuwa dala 5,000.

“A nan Najeriya, GDP namu ya ragu daga dala biliyan 500 zuwa dala biliyan 200, kuma kudaden shiga na kowane mutum ya ragu daga $ 3,500 zuwa kasa da $ 2,000 – wannan shine bambanci,” in ji shi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *