NAZIRU HAMISU.
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan.
A cikin sabon littafin sa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya.
A cewar sa wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.
Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar gargajiya domin tana taka rawar gani a ci gaban ƙasa.
Har ila yau, ya gargaɗi shugabanni cewa idan ba su magance matsalolin da jama’a ke fuskanta ba, hakan na iya haifar da rikici a nan gaba.
Leave a Reply