Ibrahim A makama
Tsohon gwamnan Jigawa, Alh Sule Lamido ya ce shugabanci ba a yinsa a cikin fushi ko haushi ko wani buri na son zuciya.
A cewarsa ana shugabanci ne cikin hakuri da hangen nesa da yin abu domin neman zaman lafiyar mabiya da kuma kasa baki daya.
“Idan ka ce za ka yi amfani da fushin ka don biyan wata bukata, ba za ka taba hukunci kan gaskiya ba sai don son ranka”
Ya ƙara da cewa “Ba za a yaƙe shi ba kan ko don ya ɓata min rai, ko don ina jin haushinsa ko don ramuwa, don ya san maganin fushi,” in ji Sule Lamido.
A cewarsa “abin da ya kamata a yi shi ne a sa kishin kasa a gaba, maimakon nuna fushi da wani”
“A yi tafiyar a matsayin nuna kasa a idon duniya ba ta tafiya daidai, sannan mulkin da ake yi a Najeriya ba a kyauta wa haƙƙin dan’adam da zaman lafiyarsa ba a yin daidai.”
Tsohon gwamnan na Jigawa na hannunka me sanda ne kan zargin da ake wa Malam Nasiru na ficewa daga APC sakamakon fushi da yayi na rashin samin kujerar minista a gwamnatin Tinubu
Alh Sule Lamido ya kuma mai da martani kan gayyatar da Malam Nasir El-Rufai yayi musu na su bar PDP su taho sabuwar Jam’iyyarsa ta SDP, inda yayi kakkausar suka kan yadda Malam Nasiru ke nuna wa Jamiyyu da dattijan Arewa Butulci, inda ya ce babu abinda Malam Nasiru ya samu ba albarkacin PDP ba, amma ya barta , yanzu kuma yana kiran wasu da su barta. Alhaji Sule Lamido ya nuna takaicinsa kan yadda Malam Nasiru a yanzu yake kokarin nuna yarda da dattijantakar Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, duk kuwa da a baya ya ce babu dattijo a Arewa.
Leave a Reply