TINUBU: Yan Nigeria ku kara hakuri …

HASSAN TURAKI.
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya da su ƙara haƙuri kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin kawo ci gaba a ƙasar.
Tinubu ya ce duk da cewa gwamnatinsa mai sauraron koken jama’a ce, amma yana so a ƙara haƙuri domin akwai haske nan gaba.
Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ruwaito Tinubu yana wannan furuci ne a ranar Juma’a, yayin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar fastocin Cocin Katolika ta Catholic Bishop’s Conference of Nigeria (CBCN) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya bayyana wa malaman cocin cewa ya ɗauki matakai masu tsauri bayan ya karɓi mulki a shekarar 2023, ciki har da cire tallafin man fetur.
Ya ce damina ta yi albarka wanda hakan ya sa farashin kayan abinci yake sauka, sannan farashin man fetur ma yana sauka.
A game da batun hare-haren ta’addanci, Tinubu ya ce rashin tsaro yana shafar musulmi da kirista, inda ya ƙara da cewa matarsa kirista ce, don haka ba zai zama mai yi musu kisan mummuƙe ba.